Chadi

Deby ya yi wa Gwamnatinsa garambawul

Shugaban kasar Chadi Idriss Déby
Shugaban kasar Chadi Idriss Déby Ludovic MARIN / AFP

Shugaban Kasar Chadi Idris Deby ya yi garambawul a Majalisar ministocin sa, inda ya rage yawan su saboda abinda ya kira karancin kudin da gwamnati ke fuskanta.

Talla

Mahamat Zene Cherif, Jakadan kasar a Majalisar Dinkin Duniya shine sabon ministan harkokin waje, yayin da Djimet Arabi, mai bai wa shugaban shawara ya zama ministan shari’a.

Kasar Chadi na daya daga cikin kasashen da suka dogara da arzikin mai, amma faduwa farashin man a kasuwannin duniya ya shafi kudaden da kasar ke samu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI