Liberia

Ana dakon sakamakon zaben Liberia

Jami'an hukumar zaben Liberia sun fara kidayar kuri'un zaben shuganbancin kasar da ya gudana a ranar Talata 26, Disamba 2017.une journée de vote pour le second tour de l'élection présidentielle, le 26 décembre.
Jami'an hukumar zaben Liberia sun fara kidayar kuri'un zaben shuganbancin kasar da ya gudana a ranar Talata 26, Disamba 2017.une journée de vote pour le second tour de l'élection présidentielle, le 26 décembre. REUTERS/Thierry Gouegnon

Jami’an zabe a Liberia su na ci gaba da kidayar kuri’un da ‘yan kasar suka kada a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu da ya gudana a ranar Talata, inda aka fafata tsakanin tsohon gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Sanata George Weah, da kuma mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai.

Talla

Ana sa ran samun sakamakon zaben nan da kwanaki kadan, wanda kuma hakan zai zama karo na farko da za’a samu mika mulki daga farar hula zuwa farar hula a kasar, tun bayan shekara ta 1944.

Tuni dai jami’an da ke sanya idanu kan zaben na Liberia na ciki da wajen kasar sama da dubu daya da suka hada da Cibiyar bunkasa demokradiya ta Amurka, NDI, suka bayyana gamsuwa da sahihancin zaben, da kuma kyakkyawan tsarin gudanarwa fiye da zagayen farko, da ya gudana a ranar 10 ga watan Oktoba da ya gabata.

Kafin wannan lokacin, sai da aka samu tsaikon makwanni bakwai, a dalilin garzayawa kotu da jam’iyya mai mulki ta Unity ta yi zuwa kotu, don neman a soke zaben zagaye na biyu, wanda George Weah ya fi samun kuri’u.

Jam’iyyar ta bayyana zargin an aikata magudi da saba wasu ka’idoji yayin gudanar da zaben zagaye na farko, sai dai bayan gudanar da bincike kotun kolin kasar ta tsayarda ranar Talata 26 ga watan Disamba domin gudanar da zaben shugabancin kasar zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI