Liberia

Guterres ya bayyana farin cikinsa da zaben Liberia

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana farin cikin sa da yadda aka gudanar da zaben shugaban kasar Liberia zagaye na biyu cikin kwanciyar hankali.

Antonio Guterres
Antonio Guterres AFP/Florent Vergnes
Talla

Guterres ya bukaci tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, daya daga cikin wakilin Majalisar bada shawara ta koli a Majalisar, da ya tafi Liberia daga gobe alhamis domin ci gaba da sa ido da kuma tuntuba a madadin Majalisar.

Sakataren ya yabawa daukacin wadanda suka bada gudumawa wajen samun nasarar gudanar da zaben ba tare da matsala ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI