Liberia

Tarihin George Weah da kuma Joseph Boakai

George Weah da Joseph Nyuma Boakai
George Weah da Joseph Nyuma Boakai ©REUTERS/Thierry Gouegnon

A wani lokaci nan gaba kadan ake saran fitar da sakamakon zaben shugabancin Liberia zagaye na biyu da aka fafata tsakanin fitaccen tsohon dan kwallon kafa George Weah da kuma mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai.

Talla

Muhimman abubuwan da ya kamata a sani kan ‘yan takaran biyu.

Tarihin George Weah

George Manneh Weah kamar yadda ake kiransa a Liberia, ya taso ne yankin Clara daya daga cikin kazaman unguwanni masu fama da talauci a birnin Monrovia kuma kakarsa mai suna Emma Klonjlaleh, ita ce ta reni har zuwa lokacin da ya shahara a shekarar 1990 a fannin kwallon kafa.

Tsohon dan wasan wanda ya taba lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya, ya yi kokarin amfani da matsayinsa wajen samun karbuwa a wurin mutanen Liberia.

Shi ne dan wasan Afrika na farko da ya lashe kyautar Ballon d'Or, kuma ya taka leda a manyan kungiyoyin kwallon kafa na Turai da suka hada da PSG da AC Milan da Monaco da Manchester City tsakanin 1989 zuwa 2003, wato lokacin da kasarsa ta Liberia ke fama da yakin basasa.

Siyasa

Weah mai shekaru 51 kuma dan kabilar Kru ya ajiye karatu a lokacin kuruciyarsa amma daga bisani ya samu kwalin digiri bayan ya sha matsin lamba daga ‘yan adawa da ke cewa, ai bai kammala karatu ba, abin da ya sa suke ganin bai shirya zama shugaban kasa ba.

Da dama daga cikin mutanen Liberia musamma matasa na matukar nuna kauna ga Weah saboda rawar da ya taka wajen tallafa musu bayan fama da yakin basasa.

A shekarar 2005 ya fara bayyana sha’awarsa ta tsayawa takarar neman kujerar shugaban kasa, sai dai ya sha kashi a hannun Ellen Johnson Sirleaf, sanna ya sa ke tsayawa a takara a 2011 duk da haka bai kai labara ba.

Weah wanda yanzu Sanata daga yankin Montserado ne ya sake shiga a dama da shi a zaben shugabancin Liberia.

Tsohon dan wasan na da yara uku kuma a can baya ya taba komawa addinin Islama daga Kirista amma daga bisani ya sake sauya sheka.

Tarihin Joseph Boakai

Joseph Nyumah Boakai mai shekaru 73, fitaccen dan siyasa ne a Liberia, kuma ya shafe tsawon shekaru 12 a matsayin mataimakin shugabar kasa.

An haifi Boakai a wani kauye da ke yankin Lofa na Liberia kuma ya taso ne cikin talauci, yayin da mahaifiyarsa ta yi fama da nakasa, abin da ya sa ya nemi hanyar daukan dawainiyar rayuwarsa da kansa.

A lokacin rayuwarsa ta neman ilimi kuwa, Boakai ya yi aikin goge-goge don samun kudin biya wa kansa makaranta, kuma ya yi nasara wajen samun nagartaccen ilimi.

Siyasa

Boakai ya rike mukamai na gwamnati da dama da suka hada da ministan ayyukan gona daga shekarra 1983-1985, wato lokacin mulkin Samule Doe da aka yi kisan gilla.

Boakai ya hadu da dan shugabar kasar mai-ci, Ellen Johnson Sirleaf a jami’a, yayin da a yanzu aka fahimci cewa akwai tsamin dangantaka tsakaninsa da Sirleaf, inda wasu ke cewa, hakan ne ya sa ta ke nuna alamar goyon baya ga babban dan adawarsa, wato George Weah.

Boakai dai, mai bin akidar Baptism ne a addinin Krista kuma yana da mata da 'ya'ya 4 da suka hada da maza uku da guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.