Kungiyar Kasashen Yammacin Afrika ECOWAS, ta yaba da yadda zaben shugabancin Liberia ya gudana cikin kwanciyar hankali, wanda George Weah ya yi nasara. A zantawarta da Abdurrahman Gambo a birnin Monrovia, Kwamishiniyar sashin kula da al'amuran siyasa, zaman lafiya da tsaro ta kungiyar, Hajiya Halima Ahmed ta jinjina wa shugabar kasar mai barin gado, Ellen Johnson Sirleaf.