Isa ga babban shafi
Gabon

Gwamnatin Gabon ta gargadi malaman addinin Islama

Yan Sanda masu bincike a yayinda suka kai samame a wata kasuwa dake birnin Libreville
Yan Sanda masu bincike a yayinda suka kai samame a wata kasuwa dake birnin Libreville Steve JORDAN / AFP
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
Minti 2

Mahukunta a kasar Gabon sun bukaci malaman addinin Islama a kasar da su ja hankulan mabiyansu domin kauce wa tashin hankali, makonni biyu bayan da wani da aka bayyana shi da cewa dan Nijar ne ya kai hari ta hanyar amfani da wuka a kan ‘yan kasar Danemark a birnin Libreville.

Talla

Hukumomin kasar ta Gabon sun bayyana cewa ana tsare da wasu mutane, akasarin wadanda aka kame, bayan samamen da jami'an tsaron suka kai kan wata kasuwa a Libraville, Hausawa ne da suka shafe tsawon lokaci suna hada-hada.

Rundunar ‘yan sandan Gabon ta ce, mutumin ya shaida mata cewa ya kai harin ne don maidawa Amurka Martani, bisa goyon bayan mai da birnin Kudus babban birnin kasar Isra’ila.

Ministan cikin gidan kasar Lambert Noet Matha, wanda ya fitar da wannan gargadi a yau juma’a, ya ce sakamakon binciken da suka gudanar na nuni da cewa wanda ake zargin ya kai harin ne ta gaban kansa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.