Cutar kwalara-Gwamnatin Zambia ta nemi agaji daga sojoji
Wallafawa ranar:
Shugaban ƙasar Zambia Edgar Lungu ya buƙaci sojoji su taimaka wajen kawo ƙarshen yaɗuwar cutar kwalara, wadda ya zuwa yanzu ta hallaka mutane 41 a ƙasar.
A cikin sanarwar da ya fitar, shugaban ya ce ya umurci ɓangarori 3 na dakarun ƙasar su haɗa hannu da ma’aikatar lafiya ta ƙasar domin rage yaɗuwar cutar a babban birnin ƙasar da kuma sauran yankuna.
Tun bayan ɓullar cutar a watan Satumba, a cewar shugaban ƙasar akan samu mutane 60 da ke kamuwa da cutar a kowace rana.
Kwalara cuta ce da ake samun ta daga ruwa mara tsafta, wadda ke da saurin yaɗuwa, kuma an fi alaƙanta ta da yankunan mutane marasa galihu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu