Bakonmu a Yau

Majalisar Dinkin Duniya na fatar ganin an gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a Libya

Sauti 03:19
Shugaban mayakan Libya Khalifa Haftar da Firaministan Libya  Fayez al-Sarraj
Shugaban mayakan Libya Khalifa Haftar da Firaministan Libya Fayez al-Sarraj Fethi Belaid, Khalil Mazraawi/AFP

Majalisar Dinkin Duniya na aiki tukuru don ganin cewa an gudanar da sahihin zaben shugaban kasa a Libya a cikin wannan shekara, bayan al’ummar kasar na ci gaba da tururuwan yin rajista don kada kuri’a.Majalisar Dinkin Duniya na fatan samun dawwamammen zaman lafiya bayan gudanar da zaben a wannan kasa da ta tsuduma cikin rikici tun bayan hambarar da gwamnatin Muhammar Gaddafi a shekararr 2011.

Talla

A halin yanzu dai kasar ta rabu gida biyu, in da kowanne bangare ke kallon kansa a matsayin halastaccen gwamnati.

A game da wannan ne Abdurrahman Gambo Ahmad ya tattauna da Kabiru Danladi Lawanti, malami a Jami’ar A.B.U da ke Zari’a a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.