Mali

Ana gudanar da zaman makoki a Mali

Wasu bakin haure a kan hanyar su ta zuwa Turai
Wasu bakin haure a kan hanyar su ta zuwa Turai REUTERS/Hani Amara

Ana gudanar da zaman makoki na kasa baki daya a Mali, sakamakon mutuwar ‘yan asalin kasar akalla 48 da ke kan hanyarsu ta zuwa Turai, yayin da wasu 69 suka samu raunuka.

Talla

Matsalar kwararar baki daga Afirka zuwa Turai duk da hatsarin da ke tattare da irin wannan tafiya, lamarin da ya kamata a ce shugabannin kasashen Afirka sun dauki mataki domin shawo kansa .

A makon da ya gabata dai hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwar ta kan yadda hukumomin birnin Roma na kasar Italiya suka kori wasu baki 800 ‘yan asalin kasashen Habasha da Eritrea

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.