Jami'an tsaron Tunisia sun cafke karin mutane 150
Wallafawa ranar:
Jami’an tsaron Tunisia sun sake kame Karin mutane 150, ciki har da ‘yan jam’iyyun adawa, yayin da dubban ‘yan kasar ke cigaba da zanga-zangar adawa da matakin gwamnati na kara yawan kudaden haraji, da kuma na kayan masarufi.
Zuwa yanzu akalla mutane 800 kenan jami’an tsaron na Tunisia suka kama cikin wannan mako.
A ranar Litinin zanga-zangar da ta juye zuwa tarzoma ta bazu zuwa sassan kasar, lamarin da ya haddasa kone gine-ginen gwamnati masu yawan gaske, hakan kuma yasa gwamnati aikewa da sojoji domin murkushe tarzomar.
Har yanzu dai akwai sauran rina a kaba, kasancewar ‘Yan adawa da kungiyoyin fafutuka, sun yi kira ga dubban ‘yan kasar da su gudanar da wata gagarumar zanga-zangar a babban birnin kasar Tunis, a gobe Lahadi.
Ranar zata zo dai dai da cika shekaru 7 da kawar da gwamnatin shugaba Zinel-Abidine Ben Ali, shugaban kasar Larabawa na farko da 'yan kasarsa suka gudanar da gagarumar zanga-zangar da ta yi sanadin rushe gwamnatinsa a shekarar 2011.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu