Turai

Ƙungiyar HRW ta gargaɗi ƙasashen Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na tattaunawa da bakin-haure.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na tattaunawa da bakin-haure. REUTERS/Michel Spingler

Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Human Rights Watch Kenneth Roth ya gargaɗi ƙasashen Turai da su daina mayar da baƙin-haure ƴan asalin Afirka daga ƙasashen Turai zuwa Libya.

Talla

‘Yanda ake cin zarafin baƙin-haure a Libya abin ya munana, ana tursasa masu yin bauta, ana tursasa masu yin karuwanci, ana azabtar da su’ in ji Mista Roth.

Shugaban na ƙungiyar ya yi bayani ne bayan da ƙungiyar ta fitar da rahoton abubuwan da suka faru a bara, wadanda suka shafi cin zarafin bil’adama.

Ya ƙara da cewa ‘Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta ce baƙin-haure da ke mutuwa a cikin ƙasar Libya sun zarta waɗanda ke mutuwa a teku lokacin da suke yunƙurin tsallakawa. Wannan manuniya ce kan munanar al’amura.’

Aƙalla mutane 3,100 ne suka hallaka a teku sa’ilin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa ƙasashen Turai daga Libya a shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.