Sudan ta Kudu

Sama da yara dubu 250 suna cikin masifar yunwa a Sudan ta Kudu

Dubban kananan yara suna cikin masifar yunwa a Sudan ta Kudu
Dubban kananan yara suna cikin masifar yunwa a Sudan ta Kudu AP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da kananan yara dubu 250 ne kasar Sudan ta Kudu, ke fuskantar hadarin hallaka, sakamakon fama da matsalar rashin abinci mai gina jiki.

Talla

Henrietta H Fore, daraktar hukumar ta UNICEF, ta yi wannan gargadin ne a jiya, yayin ziyarar kwanaki biyu da tai wasu yankunan kasar Sudan ta Kudun inda yakin basasa ya fi shafa.

Yakin da a yanzu ya shiga shekara ta 5, ya tilastawa dubban manoman kasar kauracewa ayyukansu.

Hukumar UNICEF ta ce akalla kananan yara miliyan 2.4 yakin Sudan ta Kudu, ya tilastawa tsarewa, sama da 2,300 suka hallaka, yayinda aka tilastawa akalla kananan yaran dubu 19,000 shiga aikin soja.

Kazamin yakin basasar ya fara ne cikin shekarar 2013, a lokacin da shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa, kuma madugun ‘yan tawaye Riek Machar, da yukurin yi masa juyin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.