Mali

An hallaka sojojin Mali 10 a Timbuktu

Wasu sojojin Mali, yayin da suke sintiri a babban birnin kasar Bamako. 22, Nuwamba, 2015.
Wasu sojojin Mali, yayin da suke sintiri a babban birnin kasar Bamako. 22, Nuwamba, 2015. Issouf Sanogo/AFP

Rundunar sojin kasar Mali ta ce an hallaka jami’anta 10, a wani hari da wasu mayaka masu da’awar jihadi suka kai, kan sansaninsu a Soumpi da ke yankin Timbuktu.

Talla

Majiyar rundunar sojin Mali, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mayakan sun kai harin ne da safiyar yau Asabar, inda suka jikkata wasu sojojin 17.

Harin dai ya zo ne kwanaki biyu bayan da wasu fararen hula 26 cikin har da jarirai suka hallaka, bayan taka wata nakiya da aka binne da motarsu ta ta yi a garin Boni da ke tsakiyar kasar ta Mali.

Kungiyoyin mayaka masu da’awar jihadi da ke alakanta kansu da Al-Qaeda, suna dada kai hare-hare a sassan Mali akai-akai kan sojojin kasar da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.