Mali

An sake hallaka sojojin Mali 4

Wasu sojojin kasar Mali, yayin da suke taimakawa 'yan uwansu da wasu 'yan bindiga suka hallaka, a harin da suka kai wa sansaninsu.
Wasu sojojin kasar Mali, yayin da suke taimakawa 'yan uwansu da wasu 'yan bindiga suka hallaka, a harin da suka kai wa sansaninsu. AFP

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka sojojin kasar Mali 4, a yankin Menaka da ke gabashin kasar.

Talla

Rundunar sojin Mali ta ce da safiyar wannan Lahadin dan kunar bakin waken ya dumfari wata cibiyar sojoji, sai dai kafin ya kai ga karasawa suka bude mishi wuta, tarwatsewar bam din jikinsa ne kuma ya yi sanadin hallakar sojoji 4.

Harin yazo ne kwana guda bayan da wasu mayaka masu da’awar jihadi suka hallaka sojojin na Mali 14 a harin da suka kai wa barikinsu a Soumpi da ke yankin Timbuktu.

A makon da ya gabata ne wasu fararen hula 26 cikin har da jarirai suka hallaka, bayan taka wata nakiya da aka binne da motarsu ta yi a garin Boni da ke tsakiyar kasar ta Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.