‘Najeriya ta mika shugabannin ‘yan aware Kamaru’

'Yan sanda na aikin sintiri a yankin 'yan awaren Kamaru
'Yan sanda na aikin sintiri a yankin 'yan awaren Kamaru STR / AFP

Gwamnatin Kasar Kamaru ta tabbatar da cewar Najeriya ta mika mata shugaban ‘Yan awaren kasar Sisuku Ayuk Tabe da ta tsare tun ranar 5 ga wannan watan.

Talla

Ministan sadarwa kuma kakakin gwamnati Issa Tchiroma Bakary ya ce yanzu haka Mista Tabe tare da wasu magoya bayansa 47 na tsare a hannun gwamnati.

Mista Tchiroma ya ce ”Kamaru da Najeriya abokan juna ne kuma dayansu bai yadda da duk wani matakin tada zaune tsaye ba.”

A farkon watan Janairu nan ne hukumomin Najeriya suka tsare shugaban ‘yan awaren da wasu magoya bayan sa 9 a Abuja.

Kungiyar Amnesty International ta bayyana damurta matuka a game da bukatar Kamaru wajen mika wadannan mutane, wadda ta ce ba za a yi musu adalci ba a shari’a.

Sisiku dai na bukatan yankin ‘arewa maso yammaci da kuma kudu maso yammacin kamaru masu Magana da harshen turancin Inglishi su bale daga kamaru, inda a ranar 1 ga watan Oktoba 2017, ya ayyana yankin a matsayin mai-cin gashin kanta da ya yi mata lakabi da Ambazoniya.

Kazalika tun daga wannan lokaci ake samun rikici da hare-hare ga takwarorinsu masu amfani da harshen Faransanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.