Senegal

Macron zai kafa gidauniyar tallafawa Ilimi a Senegal

Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron. REUTERS/Max Rossi

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Senegal Macky Sall, zasu jagoranci kaddamar da wata gidauniya yau a Dakar domin tara kudin tallafawa aikin bada ilimi ga yara.

Talla

Wani rahotan Majalisar Dinkin Duniya, ya ce jahilci a tsakanin matasa ya ribanya har sau uku a kasashen da suke fama da yaki ko kuma annoba, yayin da mata da yara kanana suka fi fuskantar matsalar.

Alkaluman da Majalisar ta gabatar sun nuna cewar, kusan yara 3 daga cikin 10 dake tsakanin shekaru 15 zuwa 24 a kasashen dake fama da yaki na fama da jahilci.

Alkaluman sun kuma bayyana Jamhuriyar Nijar a matsayin kasar da tafi fama da yara marasa ilimi, saboda yadda kashi 76 na matasan ta masu shekaru 15 zuwa 24 basa iya karatu da rubutu.

Majalisar tace kasashen Chadi da Sudan ta kudu da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dake fama da tashin hankali na dauke da matasa jahilai tsakanin kashi 64 zuwa 69, wanda ke nuna cewa kowanne yaro guda daga cikin 4 ba ya iya karatu a Afirka-kudu da Sahara, inda ake dauke da yara miliyan 33 da basa zuwa makaranta.

Majalisar ta bayyana jahilci a matsayin abinda ke haifar da rashin aikin yi, sanya matasa zuwa ayyukan ta’addanci da kuma kaura zuwa Turai.

Alkaluman sun nuna cewar mutane miliyan 750, basu da ilimi a duniya, kuma kashi biyu bisa uku mata ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI