Senegal: Taron bunkasa ilimi zai tallafawa yara miliyan 870

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugaban kasar Senegal Macky Sall, a birnin Dakar. Fabarairu, 2, 2018.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da shugaban kasar Senegal Macky Sall, a birnin Dakar. Fabarairu, 2, 2018. REUTERS/Ludovic Marin/Pool

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya dora alhakin karuwar tsattsauran ra’ayi na siyasa da addini a sassan duniya bisa rashin wadatar ilimi musamman a tsakanin matasa da kuma kananan yara a kasashe masu tasowa.

Talla

Macron ya bayyana haka ne yayin jawabin da ya gabatar a taron bunkasa ilimi, ranar Juma’a a Dakar babban birnin kasar Senegal, inda ya yi alkawarin bayar da gudunmawar euro miliyan 200 don tallafawa gidauniyar samar da ilimi ta kasa da kasa da aka kafa.

Taron na masu ruwa da tsaki kan samar wa da kuma inganta ilimi, ya mayar da hankali ne kan samar da hanyoyin tallafawa ilimantar da kananan yara miliyan 870 a kasashe masu tasowa 65.

Gidauniyar na neman akalla dala miliyan $3.1 domin aiwatar da tsare-tsaren fara tallafawa samar da ilimi a kasashen masu tsowa, cikin shekaru 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.