Wasanni

Tsohon mai tallafawa 'yan tawaye ya samu matsayi a hukumar CAF

Patrice Edouard Ngaissona, Tsohon ministan matasa da wasanni na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, a zamanin gwamnatin Francois Bozize, wanda ake zargi da tallafawa kungiyar 'yan tawaye ta Anti-Balaka Kiristoci.
Patrice Edouard Ngaissona, Tsohon ministan matasa da wasanni na Jamhuriyar Afrika ta tsakiya, a zamanin gwamnatin Francois Bozize, wanda ake zargi da tallafawa kungiyar 'yan tawaye ta Anti-Balaka Kiristoci. ISSOUF SANOGO/AFP/Getty

Hukumar kula da kwallon kafa ta Nahiyar Afrika CAF, ta zabi Patrice Edouardo Ngaissona, wani tsohon jagoran mayakan ‘yan tawayen Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a matsayin memba a kwamitin zartawar ta.

Talla

CAF ta cimma wannan matsayar ce, yayin taronta a kasar Morocco.

Ngaissona, tsohon minista ne na matasa da wasanni na Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a zamanin gwamnatin Francois Bozize, wanda ake zargi da tallafawa kungiyar 'yan tawaye ta Anti-Balaka Kiristoci da ke yakar kungiyar 'yan tawayen Seleka Musulmi da suka kifar da gwamnatin Bozize.

A shekarar 2015, aka haramta mishi tsayawa takarar shgabancin Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, saboda zarginsa da ake da aikata laifukan yaki a kasar, zargin da har yanzu yake musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.