Najeriya-Kamaru

An gurfanar da Najeriya kan mika 'yan aware

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Takwaran aikin sa na Kamaru Paul Biya yayin wata ganawar su a Abuja.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Takwaran aikin sa na Kamaru Paul Biya yayin wata ganawar su a Abuja. Photo: Stringer/AFP

Kungiyar da ke fafutukar kare hakkin wadanda aka ci zarafin su ta SERAP ta gurfanar da gwamnatin Najeriya da Kamaru a gaban kungiyar kasashen Afrika AU dangane da abinda ya shafi yan-aware na kasar Kamaru.

Talla

Kungiyar ta kai kasashen ne a kokarinta na ganin an kawo karshen cin zarafin yan gudun hijirar Kamaru da ke Najeriya, da kuma yadda aka tasa keyar shugabannin su da karfi zuwa gida.

Kungiyar ta bukaci AU ta yi zama na musamman kan yadda gwantin Najeriya ta mika wa gwamnatin Kamaru yan gudun hijira 51 da suka tsere wa kasarsu saboda tursasa masu da gwamnati ke yi.

Sanarwa da mataimakin daraktan kungiyar a Najeriya Timothy Adewale ya sanya wa hannu ta bayyana cewa dokar duniya ta yi bayani karara kan hakkin jama’a da masu neman mafaka da wadanda suka bar kasarsu saboda yadda ake azabtar da su.

Tun bayan da Gwamnatin Najeriya ta mika wa kamaru shugabannin 'yan awaren ne, abin ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam da ma masana harkokin kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI