Isa ga babban shafi
Najeriya

Bankunan Najeriya za su fara aiki da fasahar CRS

Babban bankin Najeriya CBN da ke Abuja babban birnin kasar.
Babban bankin Najeriya CBN da ke Abuja babban birnin kasar. ©George Osodi/Bloomberg via Getty Images
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu | Nura Ado Suleiman
Minti 1

Bankuna a Najeriya na daf da fara amfani da fasahar zamani, ta ake wa lakabi da CRS, da za ta ba su damar samun cikakkun bayanai kan asusun ajiyar kudaden manyan attijirai da kuma sauran masu biyan kudaden haraji ga gwamnatin kasar.

Talla

Fasahar wadda manyan kasashen duniya da hukumomi kamar Amurka da kungiyar tarayyar turai suka fara aiki da ita, tana taimakawa bankuna kasashen duniya wajen musayar muhimman bayanai kan masu biyan haraji, a wani yunkuri na kawo karshen matsalar kaucewa biyan kudaden harajin.

A watan Agustan shekarar bara Najeriya ta rattaba hannu kan shiga tsarin, a karkashin kungiyar bunkasa hulda da ci gaban tattalin arziki tsakanin kasashen duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.