Tanzania

Tanzania ta janye daga shirin bai wa 'yan gudun hijira agaji

Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli.
Shugaban kasar Tanzania John Pombe Magufuli. REUTERS/Sadi Said

Shugaban Tanzania John Magufuli, ya ce kasarsa zata fice daga cikin shirin majalisar dinkin duniya, wanda a karkashinsa ake bai wa ‘yan gudun hijira agajin wajen zama kayan abinci da kuma magunguna, baya ga shigar da su cikin sauran al’ummar yankin da aka karbe su.

Talla

Shugaba Magufuli ya ce Tanzania zata janye daga cikin shirin ne, bisa dalilan da suka shafi, tsaro da kuma rashin kudi.

An dai dauki tsawon lokaci ‘yan gudun hijira daga kasashen Burundi, da kuma Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na kallon kasar Tanzania a matsayin tudun mun tsira.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta gindaya sharadin cewa, dole ne duk wata kasa da ke karkashin shirin ta bai wa 'yan gudun hijirar damar samun ayyukan yi, da kuma koya musu kananan sana'o'i domin dogaro da kansu.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI