DRC

Mutane dubu 200 sun rasa gidajensu a Congo

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla 'yan gudun hijira  dubu 22 daga Congo suka tsallaka Uganda domin samun mafaka.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla 'yan gudun hijira dubu 22 daga Congo suka tsallaka Uganda domin samun mafaka. MONUSCO/Anne Herrmann

Hukumomin jinkai a Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce, akalla mutane dubu 200 suka rasa matsugunansu a yankin Ituri sakamakon tashin hankalin da ke da nasaba da kabilanci.

Talla

Wata kungiya ta ce, akalla mutane 800 ke isa Bunia kullum domin samun mafaka bayan guje wa tashin hankalin da ake samu tsakanin mutanen Hema da Lendu.

'Yan kabilar Hema dai makiyaya ne, yayin da Lendu kuma manoma ne, amma tashin hankalin da ake samu a tsakaninsu tun daga shekarar 1999 zuwa 2003, ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma dubban dabbobi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, akalla 'yan gudun hijira  dubu 22 daga Congo suka tsallaka Uganda domin samun mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.