Isa ga babban shafi
Liberia

Ana zargin wani tsohon Kanal da yi wa al'ummar Liberia kisan gilla

Wasu daga cikin mutanen da suka tsira da rayukansu a harin kisan gillar da sojojin Liberia suka kai kan wata Mujami'a a lokacin yakin basasar kasar.
Wasu daga cikin mutanen da suka tsira da rayukansu a harin kisan gillar da sojojin Liberia suka kai kan wata Mujami'a a lokacin yakin basasar kasar. Financial Express
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Wasu mutane 4 da suka tsira da rayukansu a wani hari kan wani Coci a Liberia, da akalla mutane 600 suka hallaka, a lokacin yakin basasar kasar, sun shigar da kara a watan kotu a Piladelphia da ke Amurka kan mutumin da suke zargi da bada umarnin kai harin.

Talla

Ana zargin Moses Thomas da bada umarnin kisan gillar ne a ranar 29 ga watan Yulin shekarar 1990, yayin da yake rike da mukamin Kanal a rundunar sojin Liberia, wanda ya tsere zuwa Amurka bayan karewar yakin basasar kasar.

Tuni dai Thomas ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa na take hakkin dan adam.

Kisan gillar da aka yi ma masu ibada a Mujami’a da ke Monrovia, daya ne daga cikin mafi munin laifukan yaki da aka tafka a yakin basasar Liberia da ya shafe shekaru 14, kafin kawo karshensa a shekarar 2003.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.