Afrika ta Kudu

Ramaphosa ya sha alwashin yakar cin hanci da nuna wariya

Jawabin sabon shugaban kasar Afrika ta kudun Cyril Ramaphosa na farko a gaban majalisar ya ja hankalin da dama daga cikin mambobin majalisar.
Jawabin sabon shugaban kasar Afrika ta kudun Cyril Ramaphosa na farko a gaban majalisar ya ja hankalin da dama daga cikin mambobin majalisar. REUTERS/Mike Hutchings

Sabon Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya bayyana cewar kasar za ta bude wani sabon babi wanda zai yi watsi da matsalolin da aka samu a baya, domin ginawa kasar makoma mai kyau.

Talla

Yayin da yake jawabin sa na farko a zauren Majalisa, shugaba Ramaphosa ya bayyana manufofi da dama da gwamnatinsa za ta mayar da hankali akai da suka hada da yaki da cin hanci da rashawa, gina sashen ma’adinai, bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari, samarwa matasa ayyukan yi da kuma magance matsalar basussukan da ake bin gwamnati.

Shugaban ya kuma bayyana shirinsa na gudanar da wasu shagulgula nan kwanaki 150 don nuna murna ga cikar tsohon shugaban kasar Nelson Mandela 100 da haihuwa.

A cewarsa, dole ne su nuna girmamawa ga ranar haihuwar Nelson Mandela la'akari da irin ci gaban da ya samarwa kasar, wanda Ramaphosan ya ce akansa ne zai dora don kai kasar ga tudun mun tsira.

Ramaphosa a jawaban na sa ya sha alwashin farfado da tattalin arzikin kasar, samar da ci gaba baya ga yaki da nuna wariya, yana mai cewa gaskiya ba a launin fatar mutum take ba, kamar dai yadda ya gwada misali da tsohon shugaban kasar Nelson Mandela.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.