Kamaru

Boko Haram ta kashe mutane a Kamaru da Chadi

Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi
Mayakan Boko Haram na ci gaba da kai hare-hare a kasashen Najeriya da Kamaru da Chadi © AFP PHOTO / BOKO HARAM

Mayakan Boko Haram sun kashe fararen hula akalla biyar tare da jikkata wasu biyar a wani hari da suka kaddamar a arewacin Kamaru, in da kuma a Chadi suka hallaka sojojin kasar 2.

Talla

Rahotanni na cewa, mayakan sun tsallako ne daga makwabciyar kasar, wato Najeriya, in da suka dirar wa garin Assigashia na Kamaru a cikin daren ranar Talata.

Garin Assigashia wanda ke kan iyaka da Najeriya ya yi fama da kutsen mayakan Boko Haram a can baya.

Akalla fararen hula da sojoji dubu 2 ne kungiyar ta kashe a Kamaru bayan gwamnatin kasar ta shiga yaki da mayakanta a shekarar 2014.

A bangare guda, wasu rahotannin daga birnin N’djamaina na Chadi na cewa sojin kasar biyu ne suka gamu da ajalinsu sakamakon kwanton bauna da mayakan na kungiyar Boko Haram suka kai musu a wani yanki da ke dab da kan iyakar Najeriya.

Majiyoyin samun labarai na kasar na cewa, wannan shi ne karo na farko da kungiyar Boko Haram ta kai hari a yankin tun bayan wanda ta kai bara, in da suka kashe sojoji 9.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.