Sudan ta Kudu

Matsananciyar yunwa ta addabi Sudan ta Kudu

Kananan yara na cikin wadanda matsalar karancin abimci ta fi yi wa illa a Sudan ta Kudu
Kananan yara na cikin wadanda matsalar karancin abimci ta fi yi wa illa a Sudan ta Kudu (File | AP)

Gwamnatin Sudan ta Kudu da Majalisar Dinkin Duniya sun tabbatar da matsanancin karancin abinci da matsananciyar yunwa da ke neman cin karfin kasar.

Talla

Tun bayan shekara  daya kacal da samun ‘yancin kai shekaru 6 da suka gabata, Sudan ta Kudu ta fara tsindima cikin matsanancin karancin abinci sakamakon yakin basasan kasar.

A cewar hukumar kididdiga ta kasar, kashi 40% na mutanen kasar na iya shiga matsanancin rashin abinci.

Bayanin hukumar kididdigar na cewa, a watan jiya mutane miliyan 5.3, wato kashi 48% na jumiullar al'ummar kasar na cikin halin ha'ula'i saboda rashin abinci.

A bara kadai, mutane dubu 100 ne suka shiga cikin wani hali na rashin abinci, abin da ya lakume rayukan mutane da dama.

Wata sanarwa daga kungiyoyi uku na Majalisar Dinkin Duniya na cewa, matakan da aka dauka na taimako suka sa aka ga bayan masifar yunwar.

Shekaru 4 da aka kwashe ana yakin basasa ne dai ya haifar da wannan halin karancin abincin a fadin kasar, al’amarin da ya kai ga halin da ake ciki yanzu da ba a taba ganin irinsa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.