Tattaunawa da Ra'ayin masu saurare

Ra'ayoyin masu saurare kan taron kasa da kasa don farfado da tafkin Chadi.

Sauti 15:00
Shirin na yau ya nemi jin ra'ayoyin masu saurare kan taron kasa da kasa da ke gudana a birnin Abuja na Najeriya kan yadda za a farfado da tafkin Chadi.
Shirin na yau ya nemi jin ra'ayoyin masu saurare kan taron kasa da kasa da ke gudana a birnin Abuja na Najeriya kan yadda za a farfado da tafkin Chadi. Capture d'écran : sympl.fr

Shirin Ra'ayoyin ku masu saurare na yau Talata tare da Abubakar Isah Dandago ya baku damar tofa albarkacin bakinku kan taron kasa da kasa dangane da yadda za a farfado da tafkin Chadi wanda ke ci gaba da gudana a Abuja, matakin da idan aka yi nasara zai taimakawa fiye da mutane miliyan 10 da suka dogara ta tafkin wajen samun abinci.