Najeriya

Annobar cutar Lassa na kara tsananta a Najeriya - WHO

Tsohon shugaban hukumar NCDC Dr Nasir Sani Gwarzo ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta tashi tsaye wajen hana cin bera ko mu’amala da shi, la'akari da yadda ya ke ci gaba da yada cutar a kasar.
Tsohon shugaban hukumar NCDC Dr Nasir Sani Gwarzo ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta tashi tsaye wajen hana cin bera ko mu’amala da shi, la'akari da yadda ya ke ci gaba da yada cutar a kasar. barbaric.com

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda cutar zazzabin lassa ke ci gaba da yaduwa a Najeriya, ganin yadda aka samu mutuwar mutane 72 daga cikin 317 da suka kamu da cutar a cikin wannan shekarar.

Talla

Hukumar ta ce ya zuwa yanzu mutane dubu 2 da 845 ne suka yi mu’amala da wadanda suka kamu da cutar, yayinda yanzu haka jami’an kiwon lafiya ke sa ido akan su.

Haka zalika hukumar ta ce akwai kuma jami'an lafiya 14 daga jihohin kasar 6 da suma suka kamu da cutar ta Lassa bayan bayar da kulawar gaggawa ga marasa lafiyan da suka zo asibiti dauke da cutar.

Hukumar ta WHO ta ce abin takaici ne yadda cutar ke ci gaba da kisa a Najeriyar, ko da ya ke dai hukumar kare yaduwar cutuka ta kasa NCDC ta ce ana daukar sabbin kwararan matakai don tunkarar cutar da ke ci gaba da kisa.

Sai dai kuma tsohon shugaban hukumar Dr Nasir Sani Gwarzo ya ce ya zama wajibi Gwamnati ta tashi tsaye wajen hana cin bera ko mu’amala da shi, la'akari da yadda ya ke ci gaba da yada cutar a kasar.

Ko a shekarar 2016 ma, barkewar cutar ta Lassa a jihohi 14 daga cikin 36 da ke kasar ciki har da biranen Abuja da Lagos ta hallaka fiye da mutane 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.