Sabon rikici a Jamhuriyar Congo ya hallaka mutane 15

Wasu sojojin Jamhuriyar Congo a gaf da yankin Kiwanja da ke gabashin kasar.
Wasu sojojin Jamhuriyar Congo a gaf da yankin Kiwanja da ke gabashin kasar. Reuters

Rahotanni daga gundumar Kasai a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, sun ce akalla mutane 15, aka hallaka a wani sabon rikici da ya barke.

Talla

Shugaban lardin na Kasai Andre Kapiola ya dora alhakin harin akan mayakan Nsapu Kamwina, wadanda suka kai hari kan wasu jami’an tsaro dake sintiri.

Bayanai dai daga kauyen Lombelu na gundumar Kasai sun ce galibin wadanda aka kashe a farmakin fararen hula ne, sai kuma wani soja guda.

Rikicin yankin na Kasai ya soma ne tun lokacin da aka hallaka madugun mayakan na Nsapu a shekarar 2016, bayan da ya yi tawaye ga shugaban kasar Josep Kabila, abinda yasa magoya bayan sa ke cigaba da kai hare- haren sari ka noke.

Rikicin dai ya sanya jama’ar kauyukan Kananga da kewaye arcewa zuwa dazuka don gujewa hare-haren mayakan da suka hada da kisan gilla da kuma kone kauyuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.