Amurka-Afrika

Amurka zata baiwa wasu kasashen Afrika tallafin dala miliyan 533

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson.
Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson. REUTERS/Mohamed Azakir

Gwamnatin Amurka ta sanar da ware dala miliyan 533 a matsayin tallafi da za ta mikawa kasashen Najeriya, Habasha, Somalia, Sudan ta Kudu da kuma wasu kasashen da ke zagaye da yankin tafkin Chadi.

Talla

Sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson wanda ya sanar da shirin bada tallafin, ya ce makasudin bada tallafin shi ne magance matsalolin Fari, da kuma karancin abinci mai gina jiki a kasashen.

Najeriya da Yankin Tafkin Chadi zasu amfana da akalla dala miliyan 128, yayin da kasar Sudan ta Kudu zata amfani da akalla dala miliyan 184, al’ummar Habasha kuma dala miliyan 110.

Kasar Somalia ma na daga cikin kasashen nahiyar Afrika da Amurkan ta ware kimanin dala miliyan 110 domin tallafawa ‘yan kasar da ke bukatar taimako.

Amurka tafi kowace kasa tallafawa kasashen nahiyar Afrika da ke fama da matsalolin da suka shafi fari da kuma yaki, domin daga shekarar 2017 da ta gabata zuwa yanzu, ta tallafawa kasashen nahiyar da kusan dala biliyan 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.