Nijar

Masu adawa da dokar haraji sun mamaye tituna a Jamhuriyar Niger

Masu zanga zangar kin jinin dokar haraji ta 2018 a birnin Yamai 11-03-2018
Masu zanga zangar kin jinin dokar haraji ta 2018 a birnin Yamai 11-03-2018 PRESSE LIBRE

A yau lahadi dubun dubatar mutane ne suka gudanar da zanga zangar a birnin Yamai na kasar jamhuriyar Nijar, domin nuna rashin amincewa da sabuwar dokar haraji dake kunshe a kasafin kudin kasar na 2018. Masu zanga zangar da suka karba kiran kungiyoyin fararen hula domin kalubalantar dokar harajin da kungiyoyin suka ce ta yi hannun riga da ci gaban al’ummar kasar, sun yi ta kiran mutuwa kan dokar da suka danganta da zama ta rashin adalci.

Talla

Daya daga cikin shuwagabanin kungiyoyin fararen hular dake jagorantar zanga zangar, haka kuma shugaban kungiyar Alternative " Moussa Tchangari, a gaban mahalarta zanga zangar ta yau ya ce, ba dan suna jin dadin wannan zanga zanga da suke yi ba ne, a a ta zame masu doli ne, ganin gwamnati ba ta nuna wata alama ta son shiga tattaunawa da su kan lamarin ba.

Tun a watan Oktoba 2017 da ta gabata ne, lokacin da ake shirya kasafin kudin na 2018 wasu kungiyoyin farar hula tare da jam’iyun adawa suka gudanar da wata kasaitaciyar zanga zangar neman gwamnati ta yi watsi da dokar harajin

Kungiyoyin farar hular dai, sun zargi gwamnati da kirkirar sabin dokokin haraji da za su jefa talakawa cikin mawuyacin hali, tare da yafewa manyan kamfanoni sadarwar wayar tafi da gidanka ta salula harajin kudaden da suka zarta CEFA biliyan 20, domin tatso kudaden daga jikin talakawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.