Burundi

Nkurunziza ya saka hannu kan kudirin kiran zaben raba gardama a kasar

Pierre da matarsa Denise Nkurunziza, a ranar  13 ga watan oktoba  2017, a Bujumbura.
Pierre da matarsa Denise Nkurunziza, a ranar 13 ga watan oktoba 2017, a Bujumbura. STR / AFP

A kasar Burundi yanzu haka dai an san ranar gudanar da zaben raba gardamar da ke fuskantar suka bisa manufarsa ta baiwa shugaban kasar Pierre Nkurunziza damar ci gaba da kasancewa kan karagar mulkin kasar. 

Talla

A yau lahadi ne shugaban kasar ta Burundi ya saka hannu kan kudirin kiran masu kada kuri’a su halarci rumfunan zaben raba gardamar a ranar 17 ga watan mayun gobe.

Shugaba Pierre Nkurunziza dai ya kasance daya daga cikin shuwagabani yan kama karya a nahiyar Afrika wanda kuma bayan fargabar amfani da ko wace irin hanya wajen magance adawar siyasar da yake fuskanta daga abukan hamayarsa

Da kuma sauran talakawa dake nuna yatsa a kan mulkinsa, a shekarar da ta gabata dai ta 2017 rayukan daruruwan mutane ne suka salwanta sakamako rashin amincewa da yan adawa da al’umma suka nuna kan ta zarce da ya yi kan karagar mulkin kasar bayan kwaskwarimace kundin tsarin mulkin kasar da ya yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI