Angola

Tsohon shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos zai bar siyasa

Tsohon shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos
Tsohon shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos REUTERS/Stephen Eisenhammer

Tsohon shugaban kasar Angola José Eduardo dos Santos ya bada shawarar gudanar da taron gaggawa na jam’iyarsa, ta Mouvement populaire de libération de l'Angola (MPLA), mai mulkin kasar, domin ya tsame hannuwansa kwata kwata daga cikin harakokin siyasar kasar.

Talla

A ranar juma’ar da ta gabata tsohon shugaban kasar ta Angola da ya sauka daga kan mulkin kasar dan radin kansa, ya yi fatan ganin a watan December wannan shekara ta 2018 ko a watan Afrilu 2019 an samar da wanda zai maye gurbinsa wajen shugabancin jam’iyar da ta shafe kusan rabin karni tana mulkin kasar ta Angola, domin ya tsame kansa daga cikin harakokin siyasa

Shekaru 2 da saukarsa kan mulki dan radin kansa, bisa dukkanin alamu za a iya cewa tsohon shugaban na Angola, ya fara cika al’kawalin da ya dauka, inda a ranar juma’ar 16 ga watan Maris ya bayyana cewa daga watan Desemba wannan shekara ta 2018 zuwa Afrilun 2019 zai dau ritaya daga lamuran da suka jibanci siyasa a kasar ta Angola

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.