Isa ga babban shafi
Faransa

Sarkozy na Faransa na tsare saboda wata badakalar rashawa

Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy tareda marigayi Kanal Muammar  Gaddafi na Libya a shekara ta 2007
Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy tareda marigayi Kanal Muammar Gaddafi na Libya a shekara ta 2007 REUTERS/Patrick Hertzog/Pool/File Photo
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

A cikin watan Agustan shekarar 2016 ne mai shigar da karar birnin Paris ya bayyana aniyar gurfanar da tsohon shugaban kasar Faransa  Nicolas Sarkozy a gaban kotun, tare da wasu makarabansa  da ake zargi da karbar kudade ba  bisa  ka’ida ba, a yakin neman zabensa na shekara ta 2007.

Talla

 A shekara ta 2017 wata kotu a Farnsa ta zargi Sarkozy da tsohuwar  Jam’iyyarsa ta UMP da boye wasu kudaden yakin neman zaben shi da suka kai kudi euro miliyan 18.

Amma tsohon shugaban na Faransa ya musanta zargin inda ya ce ba ya da masaniya game da kashe kudaden da suka zarce adadin wadanda aka ware domin yakin neman zabensa.

Sarkozy dai ya sha kaye a zaben 2012 da aka gudanar wanda tsohon Shugaban kasar Francois Hollande ya lashe.

Yayinda wasu daga cikin ma`aikatan kamfanin  Bymalion suka amsa cewa tabbas wannan badakala ta auku tsakaninsu da tsohuwarJam`iyyar UMP ta Sarkozy, wasu rahotanni da  masu bincike suka samu na nuni cewa tabbas Sarkozy ya karbi milyan biyar na Euro daga tsohuwar gwamnatin Libya  a karkashin marigayi Kanal Ghadafi da suka taimaka a yakin zaben shekarar 2007.

Mista Sarkozy shi ne tsohon shugaban Faransa na biyu da ya ke fuskantar shari`a tun daga shekara ta 1958.

Nicolas Sarkozy na tsare yanzu haka a Nanterre a kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.