Isa ga babban shafi
Burkina-Faso

Ana shari'ar masu yunkurin juyin mulki a Burkina Faso

Djibril Basole tare da  Gilbert Diendere yayin wani zama a kotu kan zargin kifar da gwamnatin rikon kwarya a shekara 2015, a kasar Burkina Faso
Djibril Basole tare da Gilbert Diendere yayin wani zama a kotu kan zargin kifar da gwamnatin rikon kwarya a shekara 2015, a kasar Burkina Faso RFI
Zubin rubutu: Ahmed Abba
1 min

Kotun Soji da ke Burkina Faso ta ci gaba da zaman sauraran shari'a kan wasu mutane da ake zargi da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 2015.

Talla

Mutane 84 ne dai Kotun ke tuhuma kan zargin yunkurin kifar da gwamnatin rikon kwarya a watan Satumbar 2015, shekara daya bayan kifar da gwamnatin shugaba Blaise Compaore.

Daga cikin wadanda ake tuhumar akwai babban kwamandan askarawan da ke kare tsohon shugaban kasar Compaore, wato Janar Gilbert Diendere, da ya yi garkuwa da manyan jami’an gwamnati a wancan lokaci, kafin daga bisani masu zanga-zanga da sojoji ke marawa baya su farma barikin, in da mutane 14 suka mutu nan take,yayin da wasu 270 kuma suka jikkata a wani artabu.

Sai kuma Janar Jibril Basole, da ya kasance Ministan Harkokin Kasashen Waje a karkashin gwamnatin Campaore.

Har ila yau, ana zargin askarawan da cin amanar kasa da kuma barazana ga tsaron Burkina Faso baya ga kisan jama'a ba bisa ka'ida ba.

Ana dai kallon wannan shari'ar a matsayin gwajin dafi ga bangaren shari'a a yankin yammacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.