Equatorial-Guinea

Guinea na zargin Faransawa da yunkurin kifar da gwamnatin kasar

Shugaban kasar Guinée équatoriale, Theodoro Obiang Nguema
Shugaban kasar Guinée équatoriale, Theodoro Obiang Nguema Reuters/James Akena

Mahukunta a Equatorial Guinea, na zargin wasu Faransawa uku da hannu a yukunrin kifar da gwamnatin kasar, lokacin wani hari da sojin haya suka tsara kai wa kasar a cikin wata disambar da ya gabata.

Talla

Jakadan kasar ta Guinea a Faransa Miguel Oyono, ya bukaci Faransa ta taimaka masu a binciken da suke gudanarwa dangane da wannan lamari.

Jakadan ya ce ‘Ma’aikatar shara’a na kan gudanar da aikinta, ta hanyar tara bayanai daga wasu kasashe uku, wato Chadi, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma Kamaru kasar da ta taka rawa sosai wajen hana ‘yan bindigar cimma manufarsu’’.

 Jakadan ya ci gaba da cewa ‘’Wannan bincike ne ya tabbatar da cewa akwai Faransawa uku da ke da hannu dangane da wannan yunkuri na kifar da gwamnati, kuma an kitsa lamarin ne daga nan Faransa’’, yana mai cewa duk wanda ya taka rawa wajen kitsa irin wannan makarkashiya ta daukar makamai, hakan babban abin asha ne, kuma muna fatan Faransa za ta taimaka mana domin warware wannan batu’’.

To sai dai mutanen uku sun yi watsi da wannan zargi, inda suka musanta cewa ba su da alaka da wannan lamari da ake cewa ya faru a kasar ta Guinea.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.