Senegal

Za mu hukunta masu sace yara a Senegal- Sall

Shugaban Senegal Macky Sall
Shugaban Senegal Macky Sall REUTERS/Kim Kyung-Hoon

Shugaban Senegal Macky Sall ya sha alwashin daukar mataki kan masu sace kananan yara suna kashewa a cikin kasar, abin da yanzu haka ya jefa fargaba a cikin al’umma.

Talla

'Yan Sanda sun ce ranar Talatar da ta gabata, yara biyu aka kashe ta irin wannan hanyar, yayin da aka yi kokarin sace wasu guda biyar.

Shugaba Sall ya shaida wa tashar rediyon kasar cewar, ya bada umurni mai karfi ga jami’an tsaro da su tabbatar da gano masu aikata laifin domin hukunta su.

Iyayen yara na ci gaba da nuna fargabar barin 'ya'yansu a waje don yi wasa saboda wannan ibtila'in da ya zama ruwan dare a Senegal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.