Nijar

Shayar da Jarirai nonon uwa zalla ya samu karbuwa a Nijar

Dabi'ar ta shayar da nonon uwa zalla na ci gaba da samun karbuwa a Jamhuriyar Nijar duk da cewa dai dattajai na ci gaba da nuna adawa kan matakin.
Dabi'ar ta shayar da nonon uwa zalla na ci gaba da samun karbuwa a Jamhuriyar Nijar duk da cewa dai dattajai na ci gaba da nuna adawa kan matakin. RFIHausa

A Jamhuriyar Nijar alamu na nuni da cewa dabi’ar shayar da nonon uwa zalla ga jarirai har na watanni shidda na ci gaba da samun karbuwa a sassan kasar, duk da cewa dai a bangare guda dattijai na ci gaba da adawa da matakin.Jihar Maradi na daga cikin jihohin da suka rungumi dabi’ar matakin wanda ya haddasa gagarumin sauyi a iyalai da dama musamman ta hanyar yaki da cutar tamowa mai nasaba da karancin abinci mai gina jiki ga kananan yara.Daga Maradin ga rahoton wakilinmu Salissou Issa.

Talla

Shayar da Jarirai nonon uwa zalla ya samu karbuwa a Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI