Saliyo

Ana dakon sakamakon zaben Saliyo

Zaben kasar Saliyo zagaye na biyu
Zaben kasar Saliyo zagaye na biyu REUTERS/Olivia Acland

A yau Asabar al’ummar kasar Saliyo suka kada kuri’a a zaben shugabancin kasar zagaye na biyu, wanda aka fafata tsakanin dan takarar Jam’iyya mai mulkin kasar APC Samura Kamara da kuma jagoran ‘yan adawa na SLPP Julius Maada Bio.

Talla

Kusan mutane milyan  uku da dubu 100 suka samu yi rijista a hukumar zaben kasar Saliyo,zagayen zaben na biyu da aka samu tsaikon gundanar sakamakon karar da jam’iyyar mai mulki ta shigar bisa neman zargin an tafka magudi a zagayen farko da tayi rashin nasara a hannun Maada Bio, karar da kotu ta yi watsi da ita.

Garba Aliyu Zaria daga Freetown ya aiko mana da rahoton yadda zaben ya gudana.

Zaben Saliyo

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.