Kamaru

A kalla mutane 200 suka tsere daga yankin 'yan awaren Kamaru

Akalla mutane fiye da 200 ne suka tsere wa gidajensu sakamakon rikici da ya barke tsakani jami’an tsaro da ‘yan aware a Kudu maso yammacin kasar Kamaru.

Sakamakon tashin hankalin a yankin yan aware na masu magana da harshen Ingilishi a kasar Kamaru, mutane da dama ne suke barin gidajensu domin neman mafaka a makociyar kasar Najeriya
Sakamakon tashin hankalin a yankin yan aware na masu magana da harshen Ingilishi a kasar Kamaru, mutane da dama ne suke barin gidajensu domin neman mafaka a makociyar kasar Najeriya rfi
Talla

Mutanen sun nemi mafaka ne a yankin Litoral, da ake amfani da harshen Faransanci.

Kantoman yankin Mbanga, Armstrong Voh Buikame, ya ce mutanen da suka hada da mata da kananan yara, sun fito ne daga yankin Kumba da ke lardin Kudu maso yammacin kasar, bayan da ‘yan bindigan suka kai wa kauyen farmaki a daren Jumma’a.

Voh y ace jami’an tsaro sun yi nasarar murkushe maharan, sai dai mutanen su tsorata sakamakon karan harbe-harbe, abin da ya sa suka gudu zuwa garin na Mbanga a cikin jiragen kasa yayin da wasu ke tattaki da kafa.

Su dai yankunan biyu wato Arewa maso yamma da kuma Kudu maso yammacin kasar ta Kamaru, yankuna ne na renon Ingila, wanda ke da kasha 20 cikin dari na al’ummar kasar, amma suna ganin anyi fatali da su daga yankuna da ke amfani da harshen Faransanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI