Isa ga babban shafi
Masar

Dakarun Masar sun murkushe wani hari a yankin Sinai

Sojojin gwamnati  a yankin Sinai na kasar Masar
Sojojin gwamnati a yankin Sinai na kasar Masar REUTERS/Ministry of Defence/Handout
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

A yankin Sinai ,dakarun Masar sun yi nasar kashe wasu mayakan jihadi 14.Sanarwar sojin tace an kashe mutanen ne a lokacin da suka yi kokarin kutsa kai cikin bariqin sojoji dake yankin na Sinai.

Talla

Mai magana da yahu dakarun Masar ya bayyana cewa sojin kasar 8 ne suka rasa ran su a lokacin da mayakan suka tayar da jigidar bama-bamai .

Wasu rahotani na nuni cewa rundunar sojin kasar ta yi amfani da jirgin sama wajen halaka wasu maharan guda shida.

Ga baki daya sama da mayakan jihadi 100 ne yanzu haka dakarun Masar suka yi nasar halakawa tun bayan da suka kaddamar da yaki da kungiyar Isil a yankin na Sinai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.