Guinea-Bisseau

Jose Mario Vaz ya nada sabon Firaminista

José Mário Vaz, Shugaban kasar Guinea Bisseau
José Mário Vaz, Shugaban kasar Guinea Bisseau SIA KAMBOU / AFP

Shugaban kasar Guinee Bisseau Jose Mario Vaz ya nada sabon Firaminista mai suna Aristide Gomes,sanarwa da fadar Shugaban kasar ta fitar yan lokuta da kamala taron kasashen Ecowas da ya gudana a Togo jiya asabar.

Talla

Shugaban kasar Guinea Bisseau Jose Mario Vaz ya bayyana cewa nadin Aristide Gomes na zuwa ne bayan tattaunawa da amincewa daukacin masu ruwa da tsaki a harakar siyasar kasar.

An jima ana kai ruwa rana tsakanin yan siyasar kasar Guinea Bisseau, Shugaba Jose Mario Vaz ya dau alkawalin shirya zaben yan majalisu a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.