Isa ga babban shafi
DR Congo

DR Congo ta sallami alkalai 256 saboda cin hanci

Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta sallami alkalai sama da 250 saboda cin hanci da rashawa da kuma rashin cancanta
Gwamnatin Jamhuriyar Congo ta sallami alkalai sama da 250 saboda cin hanci da rashawa da kuma rashin cancanta REUTERS/Baz Ratner
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Ahmed Abba
1 Minti

Mahukuntan Jamhuriyar Demokradiyar Congo sun sanar da korar alkalai fiye da 256 da ake zargi da cin hanci da rashawa ko kuma rashin cancanta.

Talla

Da yake karanta sanarwar da shugaban kasar Joseph Kabila ya rattabawa hannu, a gidan talabijin din kasar, ministan shari’a, Alexis Thambwe Mwamba, ya ce, an kori alkalai 174, yayin da aka dakatar da wasu alkalai biyu da suka yi murabus, sai kuma alkali guda da aka tilastawa ritaya.

Jamhuriyar Demokradiyar Congo dai na da kimanin alkalai dubu 4 na soji da na fararen hula da suka samu aiki ta hanyar tantancewar gwamnati.

Ministan shari’ar ya kara da cewa, akasarin alkalan da aka kora, sun shiga aikin ne ba tare da samun horon aikin shari’a ba, yayin da wasu kuma ke da manufar azurta kansu, abin da ke tsindima su cikin dabi’ar cin hanci da rashawa.

Ministan ya ce, za su yi sabbin dokoki da zai tsaurara matakan daukan alkalai aiki a kasar.

Ko a shekar 2009, sai da shugaba Kabila ya kori alkalai 96 bisa zargin cin hanci da rasawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.