Jamhuriyar demokradiyyar Congo

'Yan Jamhuriyar Congo 40 sun nutse a ruwa a kokarin tserewa rikici

Hukumomin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo sun ce fararen hula 40 suka nutse a ruwa lokacin da su ke kokarin tserewa tashin hankalin da ake cigaba da fuskanta a wasu yankunan kasar.

Kawo yanzu dai adadin mutanen da rikicin ya hallaka ya kai 270 yayinda wasu dubu dari biyu kuma suka rasa matsugunansu.
Kawo yanzu dai adadin mutanen da rikicin ya hallaka ya kai 270 yayinda wasu dubu dari biyu kuma suka rasa matsugunansu. Alessio Paduano / AFP
Talla

Mataimakin Gwamnan Kudancin Ubangi, Jean Bakatoye, ya ce ya zuwa daren laraba sun yi nasarar gano gawawaki 40 daga cikin wadanda suka rasa rayukan su.

An samu barkewar fada ne tsakanin Yan Tawaye da kuma sojojin gwamnati, a wani yanki da ake kira  Dongo abinda ya tilastawa fararen hular neman mafaka.

A cewar Bakatoye tun farko dakarun sojin aka kai wa farmaki wanda ya jikkata da dama daga cikinsu tare da hallaka biyu matakin da ya tilasta musu mayar da martini.

Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta fada rikici ne tun a shekarar 2009, matakin da ya sanya sojoji karbe iko da wasu muhimman yankuna a shekarra 2010.

Kawo yanzu dai adadin mutanen da rikicin ya hallaka ya kai 270 yayinda wasu dubu dari biyu kuma suka rasa matsugunansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI