Uganda

Yan Sandan Uganda sun kai samame masallaci

Birnin Kampala na kasar Uganda
Birnin Kampala na kasar Uganda REUTERS/James Akena/File Photo

Yan Sanda a kasar Uganda sun sanar da kashe mutane 2 lokacin da suka kai hari wani masallacin da suke zargin ana amfani da shi wajen cusawa matasa tsatsauran ra’ayi.

Talla

Rundunar yan sandan tace ta kama mutane da dama a harin, yayin da kuma ta kubutar da mutane sama da 100 da suka hada da mata da yara.

Kakakin yan sandan Emilian Kayima, yace daga cikin wadanda aka kubutar ana zargin cewar garkuwa akayi da su a wajen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI