Isa ga babban shafi
Malawi

Zanga-zangar kin jinina yunkurin juyin mulki ne - Mutharika

Shugaban kasar Malawi Arthur Peter Mutharika.
Shugaban kasar Malawi Arthur Peter Mutharika. Jewel SAMAD / AFP
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 min

Dubban ‘yan kasar Malawi ne suka gudanar da gagarumar zanga-zangar kin jinin gwamnati a ranar Juma’a, irinta ta farko da aka gani a kasar tun bayan makamanciyarta a shekarar 2011.

Talla

Zanga-zangar ta gudana ne a manyan biranen kasar guda shida, karkashin jagorancin kungiyoyin fararen hula, da ke adawa da yadda al’amuran kasar suka tabar bare a karkashin shugaba Peter Mutharika, da ke shugabanci tun daga 2014.

Malawi na daga cikin kasashen duniya da ke fama da talauci, wadda kuma ta dogara matuka wajen samun taimako daga manyan kasashen duniya, da kuma kungiyoyi.

A wannan Asabar ake sa ran tsohon shugaban kasar ta Malawi Joyce Banda, wanda ke gudun hijira ta sa kai, zai koma gida, duk da cewa yana fuskantar barazanar kama shi, sakamakon zargin da ake masa na aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa, a lokacin da yake rike da ragamar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.