Isa ga babban shafi
Chadi

Majalisar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulki

Shugaban kasar Chadi Idris Deby.
Shugaban kasar Chadi Idris Deby. REUTERS
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
1 Minti

Majalisar dokokin kasar Chadi ta amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar da aka yiwa kwaskwarima.

Talla

‘Yan majalisa 132 ne suka kada kuri’ar amincewa da yiwa kundin tsarin mulkin kwaskwarima, yayinda 2 suka ki amincewa da matakin.

A karkashin sabon kundin tarin mulkin, a yanzu shugaban kasa zai yi mulkin shekaru 6 ne sau biyu, a maimakon shekaru 5 ba tare da kayyada masa wa’adin sake neman shugabancin kasar ba.

A halin yanzu dai shugaban kasar Chadi mai ci Idriss Déby yana cikin wa’adin na biyar ne bisa mulkin kasar, wanda zai kare a ranar 21 ga watan Agustan shekara ta 2021.

Bayan bayyana sakamakon kada kuri’ar majalisar bisa gyaran kundin tsarin mulkin, rahotanni sun ce wasu dandanzon ‘yan adawa sun yi yunkurin gudanar da zanga-zanga a harabar majalisar, yunkurin da bai yi nasara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.