Isa ga babban shafi
DR Congo

Ebola ta sake bulla a Jamhuriyar Congo

Cutar Ebola ta sake bulla a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, in da ta kashe mutane 17 kawo yanzu
Cutar Ebola ta sake bulla a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, in da ta kashe mutane 17 kawo yanzu appsforpcdaily.com
Zubin rubutu: Abdurrahman Gambo Ahmad | Ahmed Abba
Minti 1

Ma’aikatar Lafiya a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta tabbatar da sake bullar cutar Ebola, in da tuni ta hallaka mutane 17 a lardin Equateur da ke arewa maso yammacin kasar.

Talla

Karo na 9 kenan da ake samun bullar cutar ta Ebola a Jamhuriyar Dimokradiyar Congo tun a shekarar 1976.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce, gwaje-gwaje da aka gudanar ga majinyatar na nuna cewar 2 cikin biyar na al'ummar kasar na dauke da alamun cutar.

A wata sanarwa da WHO ta fitar, ta ce tana aiki kafada da kafada da hukumomin Congo don kawo daukin gaggawa tare da gayyato abokan huldarsu wajen shawo kan cutar.

WHO ta kuma ce, ta ware Dalar Amurka milliyon daya cikin asusun agajin gaggawar hukumar tare da aika kwararru 50 domin aiki da gwamnatin Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.