Isa ga babban shafi
Najeriya

Najeriya za ta dakatar da wasanta da Congo saboda Ebola

Tawagar 'yan kwallon Najeriya Super Eagles
Tawagar 'yan kwallon Najeriya Super Eagles Reuters/Peter Cziborra
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta ce akwai yiwuwar ta dakatar da wasan sada zumunci da zai gudana tsakanin Super Eagles da Jamhuriyyar Dimkoradiyyar Congon, matukar likitoci suka bayar da shawarar hakan sakamakon bullar cutar Ebola a kasar.

Talla

A ranar 28 ga watan nan ne dai aka tsara cewa 'yan wasan na Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo za su kai ziyara birnin Port Harcourt da ke kudancin Najeriyar don fafatawa a wasan sada zumunta gabanin fara gasar cin kofin duniya a Rasha cikin watan Yuni.

Cutar ta Ebola wadda kawo yanzu ta hallaka mutane 17 wannan ne karo na 9 da ake samun bullarta a kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo tun bayan gano ta a shekarar 1970.

A jiya laraba ne dai ma'aikatar lafiyar Najeriyar ta bukaci daukar matakan kariya ta hanyar aiwatar da gwaje-gwaje kan duk wasu mutane da suka shigo kasar daga Jamhuriyar Dimkoradiyyar Congo.

A wasu bayanai da NFF din ta fitar ta ce za ta girmama dukkanin shawarar da bangaren lafiya ya bata domin baza ta amince da sanya rayukan jama'a cikin hadari ba.

Akalla mutane 7 ne suka mutu daga cikin mutane 19 da aka tabbatar suna dauke da cutar ta Ebola a Najeriyar cikin shekarar 2014, matakin kenan da ya sanya kasar daukar tsauraran matakai kan cutar wadda ta hallaka akalla mutane dubu 11 a yammacin Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.