Saliyo

Ilimin firamire da sakadanre a Saliyo za su kasancewa kyauta a Saliyo

Julius Maada Bio, Shugaban kasar Saliyo
Julius Maada Bio, Shugaban kasar Saliyo REUTERS/Olivia Acland

Sabon shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ya ce daga watan satumba mai zuwa, ilimin firamire da kuma sakadanre za su kasancewa kyauta ga illahirin ‘yan kasar.

Talla

Shugaba Maada Bio, ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da zaman sabuwar majalisar dokokin kasar a jiya alhamis, kuma wannan na daga cikin alkawurran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

Julius Maada Bio shine shugaban 'yan adawar kasar Saliyo,  wanda ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi zagaye na biyu kamar yadda hukumar zabe ta sanar, bayan lashe kusan kashi 52 na kuri’un da aka kada, in da tuni ya sha rantsuwa a birnin Freetown.

Hukumar zabe ta kasar Saliyo ta ce Julius Maada Bio, wanda tsohon soja ne, ya lashe kusan kashi 52 na kuri’un da aka kada, abin da ya ba shi nasarar doke Samura Kamara, dan takarar Jam’iyya mai mulki, wanda ya samu sama da kashi 48 na kuri'un da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.